Rundunar sojin sama ta Operation Lafiya Dole, ta yi nasarar dakile harin da ‘yan ta’addan ISWAP suka yi shirin kai wa, sakamakon harin da rundunar sojin saman ta kai wa ‘yan ta’addan a sansaninsu da yake kilomita daya da Tumbun Gini dake tsibirin Lake Chad.
Daraktan yada labaran rundunar tsaron sojin Nijeriya, Manjo Janar John Enenche, shi ne ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis, inda ya ce sun kai harin ne a ranar Laraba.
Enenche ya ce sun samu nasarar kai wa ‘yan ta’addan ne bayan sun gama bincike ta sararin samaniya, inda suka gano sansanin na su da wadansu shugabannin ISWAP da mayakansu suke taruwa domin shirya kai hare-hare.