
- Sojojin sun kwato shanu kimanin 155 da Rago da Rakumi a jihar Zamfara.
- Sojojin da akewa lakabi da OPERATION HADARIN DAJI sun kwato shanu guda dari da hamsin da biyar da Rakumi guda daya da Rago guda daya tare da motoci kirar kanta guda sha biyu.
- Sojojin sun kwato shanun ne a yankin Magana, Jangeme da Wanke inda motocin suna kokarin kaima masu saye.
Jaridar TVCNEWS sun ruwaito Sojojin dai an damka musu alhakin kuda da zirga-zirgan Yan bindiga da masu garkuwa da mutane a tsakanin jahohi hudu wadanda suka hada da Sokoto, Zamfara, Kebbi da Katsina.
KARANTA:- Daliban da Yan bindiga suka kwashe a yawuri sun dawo gida
Sojojin sun ce Yan fara bin diddigin shanun da Rakuman ne tun lokacin da Mai shanun ya kawo masu koken sace shanun.
Abubakar Abdulkadir Jagoran Sojojin HADARIN DAJIN yace “tabbas anyi nasara wajan kwato shanu ne saboda labarai da aka samu.
Ya gara da cewa ” Sojojin sa bazasuyi kasa a gwuiwa ba wajan kawo zaman Lafiya a jahohin.
Mun soma bin kadin lamarin ne tun bayan kwana biyar da jin aukuwar lamarin. Yace munyi musu kwanton bauna ne in da muke saran zasu zo kasuwa domin sayar da shanun.
Abubakar Abdulkadir yace sun damka shanun hannun wadanda aka baiwa daman bincike don su baima masu shanun kayansa.
Daga karshen ya shawarci da mutane su rinka baiwa jami’an tsaro da labarai wadanda zasu taimaka wajan kawo karshen satar shanu dake addabar yankin.
A WANI LABARIN:- Anazargin Jami’an ƙasar Myanmar da bankawa wani ƙauye wuta.
Jaridar Aljazeera ta ruwaito cewar ranar talatar da ta gabata ne wani ƙauye me suna Kin Ma, mai kimanin mutane 800 da gidaje 200 aka wayi gari ya koma toka.
Jami’an tsaron sun bankawa kauyen wuta ne bayan gamzawa da mutanen ƙauyen sukayi da abokan aikin su, inda labari ke zuwa lamarin ya janyo mutuwar wasu tsofaffi biyu.
Lamarin dai ya janyo zanga-zanga a sassan ƙauyukan da sauran garuruwan dake ƙasar jin kadan bayan labarin aika-aikar da jami’an tsaron sukayi a ƙauyen.