By Abbas Yakubu Yaura
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Dimokaradiyyar kongo sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da sojojin kasar domin gudanar da ayyukan hadin gwiwa kan kungiyoyin masu dauke da makamai dake addabar mutanen a gabashin kasar.
“Ka’idojin ayyukan hadin gwiwa” sun tsara hanyoyin bada damar gudanar da ayyukan tawagar Majalissar Dinkin Duniya dana MONUSCO da FARDC, kamar yadda aka san sojojin Kongo, in ji su.
Babban hafsan hafsoshin sojin kasar Janar Celestin Mbala da kwamandan dakarun Majalisar Dinkin Duniya a jamhuriyar Dimokuradiyyar kongo, Afonso Da Costa ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a hedkwatar sojojin tsaron kongo a ranar Talata.
Wannan dai ya cike gurbin dogon lokaci da aka dauka don “hanyar daidaitawa a matakin aiki”, in ji Da Costa.
Yarjejeniyar dai ta zo dai-dai da farmakin da dakarun kongo da na Uganda ke kaiwa kan yan ta waye mafiya zubar da jini daga cikin kungiyoyi 122 masu dauke da makamai a yankin.
Dakarun MONUSCO na daya daga cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya mafi girma kuma mafi tsada, tare da sojoji da ‘yan sanda kusan 16,000 da kasafin kudin shekara na sama da dala biliyan 1.
Sai dai ta sha suka kan yadda take fafutukar yaki da kungiyoyin masu dauke da makamai dake addabar gabashin kasar, musamman kungiyar (ADF).
Ana danganta kungiyar ADF da kisan dubban mutane a yankin Beni da kuma tashe-tashen hankula a Kampala babban birnin Uganda, wanda Amurka ke alakantata da kungiyar IS.
A ranar 30 ga watan Nuwamba ne sojojin Uganda suka kaddamar da hare-hare a kan wuraren ADF a wani samame na hadin gwiwa da DRC, inda suka kuma jibge dakaru a gefen iyakar Kongo da Kasar Uganda.
Dakarun MONUSCO ba za ta shiga cikin wadancan ayyuka na kasashen biyu ba amma dakarun uku za su yi musayar bayanan sirri don gujewa asarar ” gobarar abokantaka “.