Mai horas da yan wasn Manchester United Ole Gunner Soljsker ya ce a yanzu haka kungiyar tana ci gaba da tattaunawa da dan wasan gaban ta Edinson Cavani kan yiwuwar tsawaita zaman sa a kungiyar.
Cavani Dan asalin Kasa Uruguay ya hade da United ne a matsayin kyauta kan kwantiragin shekara guda a farkon kakar bana, kuma tuni ya baiwa marada kunya a iya zaman nashi inda ya zura kwallaye bakwa tare da taimakawa a zura biyu cikin fafatawa ashirin da biyar da yayi wa kungiyar.
An ruwaito Dan Wasan wanda ya fi kowane dan wasa zura kwallo a kungiyar Paris St. Germain na yunkurin hadewa da kungiyar kwallon kafa ta Boca Junior na kasar Argentina jim kadan bayan wani korafi da mahaifin sa ya yi.
“Da na baya jin dadin zama a Birtaniya saboda yana son zama kusa da iyalan shi, kuma na tabbata yana son zuwa fafata wasa aynakin Amurk” cewar Luis..
“Ina ga zai iya komawa nan ba da dadewa ba, hasalima ma ina tsammanin ko a watan Yulin wannan shekara”.