Mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United wato Ole Gunner Solksjaer ya bayar da sunayen ‘yan wasan da zasu fafatawa Manchester United wasannin gasar zakarun nahiyar turai wato sabuwar kakar wasa da za afara fafatawa a shekarar nan ta 2020 kuma a wannan watan na Oktoba.
Manchester United dai ta shiga tsaka mai wuya musamman a kakar wasa ta bana ganin yadda gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila musamman a makon da ya gabata bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham ta fatattakasu daci 6 da 1 har filin wasa na OldTraford.
Hakan ya sanya Manchester United ta garzaya ta sayi ‘yan wasa guda 4 a ranar da za a rufe hada-hadar kasuwar sayen ‘yan wasa inda ta sayi Edison Cavani da Ahmad Diallo da Alex Telles da kuma Facundo Pellistri.
Ga jerin sunayen ‘yan wasan da mai horas da Manchester United ya bayar:
Masu tsaron gida akwai Lee Grant da David De Gea da kuma Dean Henderson.
Masu tsaron baya kuwa akwai Aaron Wan-Bissaka da Victor Lindelof da Eric Bailly da Luke Shaw da Harry Maguire da Alex Telles da Timothy Fosu-Mensah da kuma Axel Tuanzebe.
‘Yan wasan tsakiya kuwa sune Van De Beek da Fred da Nemanja Matic da Paul Pogba da Juan Mata da Daniel James da Jesse Lingard da Bruno Fernandes da Facundo Pellistri da Scott McTominay.
‘Yan wasan gaba kuwa sune Anthony Martial da Odion Ighalo da Edinson Cavani da kuma Marcus Rashford.