Ole Gunnar Solskjær ya ce zai iya yin koyi da Sir Alex Ferguson wajen dagewa don ganin ya fita daga matsalar da yake fuskanta a matsayinsa na kocin Manchester United har ma ya iya kai kungiyar ga nasarori.
Aikin dan kasar Norway din yana tangal tangal tun bayan da Liverpool ta yi wa United dukan kawo wuka 5-0, har gida.
Duk da cewa Solskjær ne zai jagoranci kungiyar zuwa gidan Tottenham a ranar Asabar, babu tabbacin cewa zai ci gaba da kasancewa kocinta na tsawon lokaci.
Shi ma Ferguson sai da ya rage kiris a kore shi a matsayin kocin kungiyar a shekarar 1990 bayan da ya shafe sama da shekaru 3 ba tare da lashe kofi ba, amma sai ya tsallake rijiya da baya, inda a watan mayun shekarar ya lashe kofin kalubale, har ma ya shafe shekaru 23 tare da samu nasarori da ba a taba samu ba a tarihin kungiyar.
A wata zantawa da manema labarai, Solskjær ya ce zai iya kwatanta abin da Sir Ferguson ya yi a kungiyar.