Daga: Abbas Yakubu Yaura
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress AAC, Omoyele Sowore, ya mayar da martani kan rahotannin da ke cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi; Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas; Gwamna Samuel Ortom na Benue; Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo a birnin Landan.
A ranar Alhamis ne aka ga jagororin Najeriya a cikin hotuna yayin da suke ganawa kan wasu dalilai da har yanzu ba a tantance su ba a Burtaniya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wike Da Sauran Gwamnoni Suna Yiwa PDP Aiki Ne Don Samun Nasarar Jam’iyyar – Atiku
Akwai rade-radin cewa dalilin taron na kasashen waje ba zai rasa nasaba da zaben shugaban kasa na 2023 ba.
Da yake mayar da martani, Sowore ya bayyana Obasanjo, Wike, Obi da sauran su a wurin taron a matsayin ‘yan kasa na musamman, wadanda ya ce suna samun ‘mafi yawan albashi.
A cewar Sowore, ‘yan siyasar sun yi taro ne a Landan domin yanke shawara kan makomar ‘yan kasa, inda suka ce albashin da suke karba ya zarce na ma’aikatan Najeriya a jihohi 10.
Sowore ya ci gaba da cewa kudin jiragensu na kashin kansu zuwa Landan ya zarce kasafin ilimi na wasu jihohi a cikin shekara guda.
“Ba za mu iya ci gaba da haka ba,” in ji shi a cikin Kalaman sa.
Kalamansa: “Waɗannan su ne ƴan Najeriya na musamman waɗanda ke samun mafi girman albashi! Albashin wadannan ’yan gata da suka yi taro a Landan don yanke shawarar “makomarku” ya fi na ma’aikatan Najeriya a jihohi 10 na tarayya cikin wata guda.”
“Hasali ma, kudin da suke amfani da shi wajen jigilar jirage masu zaman kansu zuwa Burtaniya ya zarce kasafin ilimi na wasu jihohi a cikin shekara guda! #Bazamu Cigaba Kamar Wannan ba.”
A wani labarin kuma Uwargidan Obasanjo Ta Bukaci Gwamnatoci Da Su Tallafawa Masu Fama Da Ciwon Sukari
Uwargidan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Misis Bola Obasanjo, ta bukaci gwamnati a dukkan matakai da su tallafa wa masu fama da ciwon suga a kasar nan.
Misis Obasanjo ta koka da cewa kudaden da ake kashewa wajen kula da ciwon suga na da yawa, inda ta kara da cewa majinyatan na bukatar taimako daga gwamnati da masu hannu da shuni.