ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sporting CP dake ƙasar Portugal ta bayyana cewar ta sauya sunan ƙaramar ƙungiyarta da sunan shahararren ɗan wasanta wanda a yanzu haka ya zama gagarabadau a duniyar ƙwallon ƙafa kuma ɗan asalin ƙasar Portugal wato Christiano Ronaldo.
Ta bayyana hakanne a wannan yammaci na Lahadi inda tace yadda take ƙyanƙyashe shahararrun ‘yan wasa Ronaldo ya cancanta ta maye sunan Academiy ɗin ƙungiyar da sunansa duba da gudun mawar daya basu kuma ya baiwa ƙasar Portugal gudun mawa da sauran ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan daya bugawa wasa.
Ronaldo dai a halin yanzu duk juyin da aka yi za a bayyana cewar daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sporting CP ya fara wadda take a ƙasar Portugal.
Ronaldo dai lokacin yana mayashin ɗan wasa ya bugawa Academy na Sporting CP daga shekarar 1997 zuwa 2002.
Haka lokacin daya fara buga wasa a matsayinsa na babban ɗan wasa ya bugawa Sporting CP B wasa a shekarar 2002 inda ya buga wasanni 2 amma baijefa ƙaallo ko guda ba.
Haka daga shekarar 2002 zuwa 2003 ya bugawa babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sporting CP inda ya buga wasanni 25 ya jefa ƙwallaye guda 3.
A yanzu dai ta tabbata cewar an sauya sunan ƙaramar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sporting CP zuwa sunan Christiano Ronaldo kuma sunan ya fara aiki daga wannan rana ta Litinin 21 ga watan Satumba na shekarar 2020.