Mambobin kwamitin hadin gwiwa na kungiyar ma’aikatan da ba ilimi ba da kuma manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya reshen jami’ar Legas na gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da dakatar da yajin aikin da shugabanninsu suka yi ba zato ba tsammani.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewa ‘yan kungiyar da suka fusata sun ce shugabanninsu ba su bi ka’ida ba kafin a dakatar da yajin aikin a ranar Asabar da ta gabata.
Kwamitin hadin gwiwar na SSANU/NASU a sanarwar da ya fitar a ranar Asabar din da ta gabata ta bukaci daukacin mambobinta na kasa baki daya da su koma yau, sai dai kungiyar UNILAG reshenta sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da dakatar da yajin aikin.
KARANTA ANAN: Yadda Turkiyya Ta Tilastawa Yan Wasan Najeriya Kwana A Filin Jirgi
A yau Laraba har kawo wannan lokacin hada rahoto, ‘yan kungiyar SSANU/NASU reshen jami’ar UNILAG, sun dauki kwalaye daban-daban dauke da rubuce-rubuce, ‘Mun gaji da babban sakatare Adeyemi Peters da Mohammed Ibrahim na SSANU, dole su tafi!’, ‘Mu ba ma’aikatan gwamnati ba ne.”
A ranar 27 ga watan Maris, gamayyar kungiyoyin suka fara yajin aikin da suka dakatar a ranar 20 ga watan Agusta.
A wani labarin kuma:
Yajin Aikin ASU Zai Ci Gaba, Don Har Yanzu FG Ba Ta Dauki Kwararan Matakai Ba