Suleiman Isah Isah, wani dan Kano wanda baturiya ta nuko gari tun daga kasarta musamman tazo har Kano don suyi aure ya wallafa hotunan cigaban da ya samu.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa inda ya sanya hotunansa biyu, na farko lokacin na shekarun baya, sai dayan kuma na yanzu da yake shanawa.
KU KARANTA: CBN ya yi ƙarin haske kan alfanun sake fasalta kuɗin Najeriya
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa:
“Su Suleimanu an ci kuɗin Baturiya an yi bulbul.”
Nan da nan mutane su ka zagara su na ta tsokaci iri-iri karkashin wallafar tasa duk da dai bisa barkwanci yayi, amma lamarin ya dauki hankula sosai.
Sanin kowa ne yadda uwargidan Shugaban kasa Muhammad Buhari, Aisha tasa aka kama wani matashi wanda yayi mata batanci.
An samu rahoto kan yadda yanzu haka yaron ke gaban hukuma yayin da ake shirin gurfanar da shi, wannan yasa mutane da dama suka dinga yin wallafa cike da barkwanci suna cewa sun ci kudi sun yi kiba.
Kuɗin kyauta, da Albashi baza su isheku rayuwa ba — Adeyanju ga Ƴan Najeriya
Dan rajin kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju ya shaidawa ‘yan Najeriya cewa kudin kyauta da albashin wata ba su isa ba ga rayuwar mutum.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su shiga sana’o’in da za su rika samun kudaden shiga akai-akai.
Adeyanju ya bayyana haka ne a ranar Asabar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.