Tsohon dan wasan Barcelona da ya koma Atletico Madrid Luis Suarez, ya goge tarihin da Cristiano Ronaldo ya kafa na cin kwallaye 16 cikin wasanni 17 a farkon kakar wasa a La Liga, abinda ya sa shi zama dan wasa mafi saurin jefawa abokan hamayya kwallon.
Yayin wasan da suka fafata a ranar Litinin, Celta Vigo ce ta soma jefawa Atletico Madrid kwallo, amma Surez ya rama ya kuma kara, sai dai daga bisani masu masaukin bakin sun sake jefa kwallo inda aka tashi 2-2, ake ganin zai yiwa Real Madrid da Barcelona dadi, ganin cewar tazarar maki 8 ya rage tsakaninsu a maimakon 10.
Cikin watan satumban shekarar 2020 Suarez ya koma Atletico Madrid bayan shafe shekaru 6 a Barcelona, inda ya ci mata kwallaye 198 cikin wasanni 283 da buga mata.
Kafin sauyin shekar dai an yi jita-jitar dan wasan zai koma wasa ne zuwa kungiyar Juventus dake gasar Seria A.