Wani Magidanci mai a Karamar Hukumar Yagba ta Gabas dake Jihar Kogi mai suna Makanjuola Ayedun ya Murkushe Matarsa da mota har lahira.
Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ne dai lamarin ya aukua karamar hukumar Gwagwalada na birnin tarayya Abuja wuraren karfe gima na dare.
Rahotanni sun bayyana cewa mutumin ya murkushe matar tasa ce wacce ma’aikaciya ce da Bankin Duniya yayin da yake ja da baya da motar tasa.
Majiyoyi da dama sun ce da gangan mutumin ya kutsa ta wata hanya wacce da ma ba hanyar bi bane lamarin da ya kai ga ya lalata kayayyakin aikin gida na dubban nairori.
Bayan da ya tabbatar da matar tasa ta cika, nan ne kuma ya nemi hanyar arcewa inda ya ce ba da gangan ya yi hakan ba, inda ya alakanta lamarin da kwacewar burki.
Wani Makusanci ga Magidantan ya bayyana cewa da ma ya jima yana musguna wa uyakin tashi.
“Lamarin ya samo asali ne bayan da ta gano cewa mijin nata ya fasa wani asusu da ta yi bikin ranar haihuwar danta, bayan ta tunkare shi da maganar ne sai cibi ya zama ƙari”
Rahotanni sun bayyana cewa da ma dai matar ita take ciyar da iyalan gidan gaba daya kasancewar nai gidan ba shi da aikin yi.