Sarki Salman na Saudiyya ya fitar da wata sanarwa ta tsawaita nadin Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais a matsayin Shugaban masallatan Harami biyu na tsawon shekara hudu.
Kafar yada labarai ta intanet ta Saudi Gazette ta ruwaito cewa Sudais ya yaba wa Sarki Salman da Yarima Muhammad Bin Salman saboda sake aminta da shi kan wannan matsayi yana mai cewa fadar na samun kulawa daga masu mulki.
”Wannan ya taimaka wa fadar wajen tafiyar da ayyukanta cikin sauki da kwarewa.
”Hakan kuma ya yi dai-dai da kulawa da kuma bibiyar harkokin tafiyar da Masallatan biyu masu tsarki da kuma masu ziyartarsu wanda ya ke biyan muradun jagoranci a kasar.”