By Abbas Yakubu Yaura
Babban hafsan sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya rattaba hannu a ranar Lahadin da ta gabata kan wata yarjejeniya da firaminista Abdalla Hamdok ya gabatar domin maido da mulkin farar hula kusan wata guda bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.
Yarjejeniyar mai kunshe da batutuwa 14 da aka rattaba wa hannu a fadar shugaban kasar dake birnin Khartoum, ta tanadi mayar da Hamdok kan mukaminsa na firaminista, da kuma sakin shugabannin farar hula.
Hamdok dai yana karkashin kulawa ne tun bayan da Janar Abdel Fattah al-Burhan ya ayyana dokar ta baci a ranar 25 ga watan Oktoba tare da hambarar da gwamnatin kasar, matakin daya kara daukar matakin mika mulkin farar hula na tsawon shekaru biyu, wanda kuma ya janyo suka daga kasashen duniya.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa An dage zaman gidan da aka yiwa Faraminista Abdalla Hamdok, kuma dakarun dake gadin gidansa sun janye,” in ji wani jami’i.
An dauki matakin ne bayan masu shiga tsakani a ranar Lahadin data gabata sun sanar da cewa sojoji sun cimma matsaya kan maido da Hamdok kan mukaminsa na Firaminista.
Komawar Hamdok, masanin tattalin arziki dan kasar Birtaniya wanda ya yi aiki da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin Afirka, ya kasance babbar bukatar kasashen duniya.
Daukar matakin hambarar da gwamnatin ya janyo zanga-zangar da aka yi a titunan kasar inda aka kashe masu zanga-zangar 40, a cewar majiyoyin lafiya.
Sai dai yayin da labarin ci gaban ya bayyana, daruruwan masu zanga-zangar sun sake yin zanga-zangar nuna adawa da sojoji da kuma murkushe masu zanga-zangar, kamar yadda shaidu suka bayyana.
Babbar kungiyar farar hula data jagoranci zanga-zangar adawa da Bashir tare da rattaba hannu kan yarjejeniyar raba madafun iko a shekara ta 2019 da sojoji ta yi watsi da yarjejeniyar ta ranar Lahadi.