By Abbas Yakubu Yaura
Dubban ‘yan kasar Sudan ne suka fito kan tituna a ranar litinin a babban birnin kasar Khartoum da kuma wasu biranen kasar a wata sabuwar zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Oktoba da kuma yarjejeniyar da ta mayar da Firaminista Abdalla Hamdok kan mukaminsa.
Hotunan dake yawo a kafafen sada zumunta sun nuna masu zanga-zangar sun yi dandazo a wurare daban-daban a birnin Khartoum da kuma garin Omdurman, An kuma gudanar da zanga-zanga a wasu garuruwa da suka hada da Kassala, Sennar da kuma Port Sudan.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Jami’an tsaro sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar da suka yi maci a wani titi kusa da fadar shugaban kasa a birnin Khartoum. Kawo yanzu dai babu rahoton asarar rayuka.
A zagayen da suka yi jami’an tsaro sun yi amfani da harsashi mai rai kan masu zanga-zangar, a cewar masu fafutuka. Akalla masu zanga-zangar 44 ne aka kashe tare da jikkata wasu daruruwa tun bayan juyin mulkin, a cewar kwamitin likitocin Sudan.
Sojojin Sudan sun kwace mulki a ranar 25 ga watan Oktoba, inda suka rusa gwamnatin rikon kwarya tare da kame dimbin jami’ai da ‘yan siyasa.
An maido da Hamdok kan aiki a watan da ya gabata sakamakon matsin lamba daga kasashen duniya a wata yarjejeniyar da ta bukaci kafa majalisar ministoci mai zaman kanta karkashin kulawar sojoji.Yarjejeniyar dai ta hada da sakin jami’an gwamnati da ‘yan siyasa da ake tsare da su tun bayan juyin mulkin da kuma kafa majalisar ministoci mai zaman kanta a karkashin jagorancin Hamdok.
Sai dai kungiyar masu rajin tabbatar da dimokuradiyya ta yi watsi da yarjejeniyar, wacce ta dage kan mika mulki ga gwamnatin farar hula domin jagorantar mika mulki. Zanga-zangar ta zo ne a karkashin taken: “Babu shawarwari, babu sulhu, ba a raba madafun iko” da sojoji.