Daga: Abbas Yakubu Yaura
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta Kudu ta ce ta kira wani jami’in diflomasiyyar ta da ke zaune a Amurka bayan “wani lamari na fyade” a birnin New York, tare da dakatar da jami’in har sai an kammala bincike.
“Abin takaici ne cewa jami’in diflomasiyyarmu ya shiga cikin wani zargin fyade da… (a) mazaunin birnin New York,” in ji ma’aikatar a cikin wata sanarwa da aka buga a shafin gwamnati na Twitter a yammacin ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’o’in Jihohi A Najeriya Basu Da Amfani – ASUU
Sanarwar ta ce “Jami’in diflomasiyyar da ake magana a kai yanzu ya dawo gida Sudan ta Kudu kuma an dakatar da shi daga aikinsa, yana jiran sakamakon wannan bincike.”
“Lalacewar jima’i a kowace irin siffa abin muni ne kuma ba za a yarda da shi ba,” in ji shi, ya kara da cewa “wani kwamiti na musamman” yana nazarin kan lamarin.”
Sanarwar ba ta yi karin haske kan zargin ba, amma kafofin yada labaran Amurka sun ce ana zargin jami’in diflomasiyyar da shiga gidan wacce abin ya shafa a Manhattan da karfi tare da yi mata fyade a ranar Lahadi.
Da farko ‘yan sanda sun tsare shi kafin su sake shi bayan sa’o’i da ya nemi kariya ta diflomasiyya.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fada a ranar Laraba cewa “tana sane da lamarin… da ya shafi wani jami’in diflomasiyya da aka amince da shi ga Majalisar Dinkin Duniya.”
“Muna daukar wadannan zarge-zargen da mahimmanci kuma muna aiki kafada da kafada da Sashen ‘yan sanda na New York da ofishin magajin gari mai kula da harkokin kasa da kasa,” in ji kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Vedant Patel, ba tare da bayar da karin bayani ba.
A cikin watan Maris, Majalisar Dinkin Duniya ta zargi mambobin gwamnatin Sudan ta Kudu da aikata laifukan cin zarafin bil’adama “wanda ya kai ga laifuffukan yaki” a yankin kudu maso yammacin kasar, inda ta bukaci a gudanar da bincike kan mutane da dama, ciki har da cin zarafin mata da cin zarafin kananan yara.
Sabuwar al’ummar duniya na fama da rashin kwanciyar hankali tun bayan samun ‘yancin kai a shekarar 2011, inda Majalisar Dinkin Duniya ta sha sukar shugabancin Sudan ta Kudu saboda rawar da ta taka wajen tada tarzoma, da murkushe ‘yancin siyasa da wawure dukiyar jama’a.
A wani labarin kuma Atiku Ya Gargadi Mambobin Jam’iyyar Su Kan Kalaman Da Ke Kawo Cikas Ga Hadin Kan PDP
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da magoya bayan jam’iyyar da su guji furta kalaman da za su iya kawo cikas ga hadin kan jam’iyyar.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai Mista Paul Ibe a Abuja.