A wani mataki na gyara tattalin arzikin kasar da yiwa tattalin arzikin kwaskwarima, kasar Sudan ta ce za ta rage darajar takardun kuɗinta.
Rahotanni sun tabbatar da cewa; a halin yanzu a kan sauya takardar kuɗin ƙasar ta fam ko jinai 55 ga kowace dalar Amurka ɗaya ne a hukumance, amma ya kan kai jinai 140 a kasuwannin bayan fage.
Matsalar hauhawar farashin kaya da kuma raguwar kuɗaɗen shiga na kashi 40 cikin 100 da gwamnati ke fuskanta a halin yanzu, ya tilasta dole a dauki wadannan matakan kamar yadda muƙaddashin ministan kuɗin ƙasar ya tabbatar.