Sufeta Janar na Yan Sanda Muhammad Adamu ya umarci jamian yan sanda da kada su yi kasa a gwiwa wajen kare kan su daga harin inyamurai a jihar Imo.
Sufeta Janar din ya yi wannan umarni ne sa’ilin da ya kai ziyarar gani da ido kan irin barnar da inyamuran suka yi a Gidan yari da Shelkwatar yan sandar jihar ta Imo.
Yayin harin na Inyamurai, daruruwan yan fursuna ne suka samu nasarar tserewa wanda harin an kai shi ne sanyin safiyar jiya Lititnin.
Kazalika yayin harin, an harbi wani dan fursuna guda a ka yayin da yake yunkurin daukar jakar shi don tserewa.
Da yake jawabi ga jamian yan sandar bayan gane wa idanun su irin ta’adin da aka yi, Sufeta Janar din ya bukaci jama’a daa su taimaka da sahihian bayanai da za su taimaka wajen gano inda yan fursuna da suka tsere suke.
Har wa yau ya umarci yan sanda da kada su ande hannu su zauna, su tashi su yi amfani da makamai wajen kare kan su daga hare-haren Inyamuran da ake kira da IPOB.
Idan za a iya tunawa dai Sufeta /janar din yan sandan ya bada umarnin kara girke jamaian tsaro don maido da doka da oda.