Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta musanta rahotannin dake cewar babban Sufeton ta Muhammad Adamu ya biya naira biliyan Biyu a matsayin tsohiyar baki domin tsawaita wa’adin ci gaba da rike mukaminsa.
Cikin sanarwar da ya fitar kakakin ‘yan sandan Nijeriya Frank Mba, ya bayyana labarin tuhumar da ake yiwa babban Sufeton a matsayin kokarin bata masa suna da wasu miyagu ke yi.
A cewar Mba abin mamaki ne da kuma takaici ganin yadda masu yada rahoton karyar suka bayyana rashin murnar kara masa wa’adi da babban Sufeton ya yi a matsayin daya daga cikin hujjojin dake tabbatar da cewa sai da aljihunsa ya ji jiki ta hanyar aman daruruwan miliyoyin Naira kafin bukatarsa ta biya.
A ranar 1 ga watan Fabarairu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karawa Sufeton ‘yan sandan kasar Muhammad Adamu wa’adin ci gaba da rike mukaminsa, matakin da Ministan kula da ayyukan ‘yan sanda Muhammad Dingyadi ya ce an dauka, domin samun damar zaben sabon shugaban rundunar ‘yan sandan cikin nutsuwa da taka tsantsan.