Bayan cimma yarjejeniya da gwamnati a jihar Katsina, masu garkuwa da mutane sun sake sakin wasu mutum 30. An mika wadanda aka sakin ne ga gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a fadar gwamnatin jihar Katsina a ranar Lahadi.
Kamfanin dillancin labarai ya labarto cewa wadanda aka saki din mutane da aka yi garkuwa da su daga garuruwan Kankara da Shimfida dake a karamar hukumar Jibiya. Bayan sace su kuma an fita da su daga jihar Katsina zuwa dajin Dan Sadau cikin jihar Zamfara, inda a nan ne ma suka shafe wasu makonni.
Gwamna Masari, a yayin tattaunawa da wadanda suka samu kubutar ya ce zai ci gaba da yin magana da ‘yan ta’adda da nufin ya tausasa zuciyoyinsu, su hakura su ajiye bindiga tare da dawo da mutanen da suka sace.
Gwamna Masari ya umurci da a kai wadanda suka kubuta asibiti don gwada lafiyarsu kafi a mayar da su ga iyalansu. Wata mata daga cikin wadanda suka samu kubuta, Zinatu sani daga garin Kankara ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun sace ta ne daga gidan mijinta tare da ‘ya’yanta biyu sannan kuma suka nemi da a biya su Naira miliyan 20 kafin su sake su.
Da iyalanta suka nuna cewa basu da halin biyan Naira miliyan 20, sai ‘yan ta’addan suka rage kudin fansar zuwa Naira miliyan 6, nan ma dai abin ya ci tira.
Zinatu ta bayyana yadda suka kwashe kwanaki 55 suna kwana a dajin Allah cikin ruwan sama da zafin rana. Ta kuma bayyana yadda ‘yan ta’addan ke bata shinkafa ta dafa babu ko mai, daga ruwa sai gishiri.