Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3, ya umarci Al’ummar Musulmi dasu duba sabon jinjirin watan Dhul Hijja na Shekarar 1442AH.
Abubakar Wanda Kuma shine Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, ya bayyana haka a ranar Juma’a a cikin wani jawabi da aka fitar.
Kamfanin Dillancin Labaru na Kasa wato-NAN ya ruwaito cewa, Shugaban Kwamitin Bayar da Shawara akan Harkokin Addinin Musulunci na Majalisar Farfesa Sambo Junaidu ya sanyawa takardar hannu.
“Muna sanar da Al’ummar Musulmi cewa ranar Asabar 10 ga watan Juli Wanda yayi dai-dai da 29 ga watan Dhul Qadah na Shekarar Musulunci ta 1442AH, itace ranar da za’a duba jinjirin watan Dhul Hijja na Shekarar 1442AH.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Sanya alamar rushe gine-gine 70 a Legas
“Ana bukatar Musulmi dasu Fara duba jinjirin watan a ranar Asabar, tare da kawo rahoton ganin da suka yi, ga Hakimi ko Dagaci mafi kusa a garesu, domin kai rahoton ga Sultan”inji shi.
Sultan yayi addu’a ga Allah daya taimaki Musulmi wajen gudanar da ayyukan Addinin musulunci.
Watan Dhu Hijja shine wata na 12 a Kalandar Musulunci, inda wannan wata,wata ne na sadaukarwa, tare da gudanar aikin Hajji da Shagulgula.
Comments 1