Babban Hafsan Sojin Najeriya Laftnar Janar Ibrahim Attahiru ya gargadi masu rajin barkewa daga Najeriyar nan Asari Dokubo da kuma takwarn shi Sunday Igboho.
Wannan gargadi na Hafsan Sojin na zuwa yayin wani taron kara wa juna sani na manyan kwamandojin sojin kasar nan karo na farko.
Idan za a iya tunawa dai a yan baya-bayan nan ne Igboho ya ayyana ballewar yankin kudu maso yamma daga kasar nan.
Kazalika shi ma Asari Dokubo ya ayyana kafa kasar Biafra inda kasar ta kunshi yankin kudu maso gabas da kuma kudu maso kudu a matsayin yankin na Biafra.
To sai dai Attahiru ya tabbatar da kakkausar murya cewa rundunar sojin Najeriya ba za ta ragar wa duk wani yunkuri na kawo barazanar tsaro a kasar nan ba musamman irin na takadarai ikamar su Dokubo da kuma Igboho.
“rundunar sojin Najeriya za ta ci gaba da nuna ba sani ba sabo, ba za ta ragar wa kowa ba muddin yana yunkurin kawo barazana ga harkar tsaron kasar na”. cewar Attahiru.
ya kara da cewa “Rundunar kazalika ta karo wulakanci ba kamar baya ba kuma tana nan kan bakar na yin maganin ko wani takadari a kasar nan, ko da kuwa wanene”.