Wani tsohon dan wasan kungioyar kwallon kafar Nigeria Super Eagles, mai buga wasan baya, mai suna Yisa Sofoluwe, ya mutu yana da shekaru 53 a duniya.
Rahotanni sun bayyana cewa, dan wasan bayan wanda ake yi wa lakani da ‘Dodon tsaron baya’ ya kamu da cutar matsalar lakka, inda ya ke jinya a asibitin koyarwa na Prince and Life da ke Ikorodu, jihar Lagos.
Sai dai daga bisani an mayar da shi babban asibitin koyarwa na jami’ar Lagos a ranar Juma’ar da ta gabata, bayan da rashin lafiyar ta sa ta tsananta.
A daren ranar Talata ne aka tabbatar da mutuwar tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafar Nigeria, Yisa.
“Mun sake rasa wani babban zakara a harkar wasan kwallon kafa, Yisa Otobo Shofoluwe, dodon tsaron baya,” tsohon dan wasan Stationery Stores kuma abokin Sofoluwe, Mr Taiwo Oloyede ya sanar a daren ranar Talata.
Sofoluwe ya buga wa Super Eagles wasanni 40 a tsawon taka ledarsa, kuma ya ci kwallo sau daya.
Ya kasance mamba na tawagar bugawa Eagles wasa da ta kai matakin wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Africa (AFCON) a shekarar 1984 da 1988.
Mutuwar Sofoluwe ta zo ne kwanaki kadan bayan sanar da mutuwar tsohon dan wasan Super Eagles, Joe Erico.