Shahararren mai kada sarewa, Tee Mac Omatshola Iseli ya bayyana dalilan da ya sa dan takarar shugaban kasa karkashin jnuwar jam’iyar APC, Bola Tinubu, bai kamata ya zama shugaban Najeriya ba.
Tee Mac yayi ikirarin cewa Tinubu yana da shekaru 86 don haka kuma bai cancanci zama shugaban Najeriya ba.
Tsohon shugaban kungiyar mawaka ta Najeriya, PMAN, ya ce shi da matar Tinubu, Remi ’yan uwa ne amma ya daina goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a 2015 saboda ya nemi ‘yan Najeriya su zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Da yake mayar da martani ga wani ma’abocin Facebook, Yemi Olakitan, wanda ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu, Tee Mac ya ce ya daina ziyartar gidan Tinubu da goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC duk da kasancewarsa suruki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kano Ta Amince Da Karin Kashi 50 Na Tallafin Karatu Ga Daliban Jihar
Ya wallafa cewa: “Ya kai Yemi, kowa zai iya zaɓar kowane ɗan takara amma mai hankali zai yi wa kansa tambayar: shin na zaɓa wanda ya dace! Shin mutumin ya cancanta? Shin mai gaskiya ne? Shin yana gaya mana gaskiya game da shekarunsa, tarihinsa, da kuma yadda ya sami kuɗinsa? Shin mutumin yana da koshin lafiya yana da shekaru 86, zaj iya ɗaukar aikin ƙasar da ta lalace gaba ɗaya?
“Ka ga, Tinubu surikina ne. Matarsa Remi ƙanwata ce, mahaifiyarta Itsekiri da mahaifiyata Itsekiri yan uwan juna ne. Na san Tinubu tun tsakiyar shekarun 80s da kaina har ma na shirya shi ya zauna a gidan ubana (SIR MOBOLAJI BANK-ANTHONY) a Landan lokacin da ya tafi gudun hijira.
“Na daina ba shi goyon baya, na daina ziyartar dangisa da sauransu lokacin da ya tallata wa al’umma shugaba Buhari a shekarar 2015.
“Don haka Ina shawartar al’umma cewa wannan mutumi bai cancanci zama shugaban mu ba” inji shi.
A wani labarin kuma na daban.
Majalisar zartaswar jihar Kano ta amince da sake duba kashi 50 cikin 100 na alawus-alawus din kudin karatu na ‘yan asalin jihar da ke karatu a makarantun Najeriya da kuma fitar da Naira miliyan 865, 449,150.00 ga hukumar ba da tallafin karatu ta jihar a matsayin fitaccen alawus da kudin kayan karatu don biyan dalibai a fadin kananan hukumomi 44 na masarautu biyar da ke jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya yi wa manema labarai karin haske kan sakamakon taron na mako-mako da aka gudanar a zauren majalisar da ke gidan gwamnati, Kano, ya bayyana cewa adadin dalibai 40,494 ne za su ci ji gajiyar tallafin.
Ya kara da cewa, jimillar tallafin karatu ga daliban cikin gida guda 40, 494 daga masarautar Karaye, Bichi, Rano, Kaya da Kano a cikin kananan hukumomi 44 na jihar ya kai Naira 836, 269, 150, yayin da kudin kayan aikin karatu ya kai naira miliyan 29,180, 000.00.
Malam Garba ya ci gaba da cewa masarautar Karaye tana da kananan hukumomi takwas da dalibai 3,094 za su samu kudaden alawus-alawus na Naira miliyan 61,463,950.00 da kuma Naira miliyan 4,020, 000.00 a matsayin kudin karatun, yayin da masarautar Bichi mai kananan hukumomi tara da dalibai 3,494 za su samu Naira miliyan 71,242, 800.00 a matsayin manyan alawus da kuma Naira miliyan 4,020.000.00 na kayan aiki.
Kwamishinan ya kuma zayyana alawus-alawus da kayan aiki ga dalibai 4,015 daga Masarautar Rano maai kananan hukumomi 10 sun kai Naira miliyan 78, 351, 800.00 da Naira miliyan 4, 02, 000.00, sai Masarautar Gaya mai kananan hukumomi tara da dalibai 4, 260 ne za su karbi Naira miliyan 86, 236, 600.00 a matsayin alawus alawus da kuma Naira miliyan 4, 02, 000.00 na kayan aiki.
Masarautar Kano, ya ce, tana da kananan hukumomi takwas na da fitattun alawus-alawus ga dalibai 26, 086, kuma za su karbi Naira miliyan 538, 974, 000.00 da kuma biyan Naira miliyan 13, 100, 000.00 na kayan aikin karatun.