By Abbas Yakubu Yaura
A jiya ne wata kotun Majistare dake Yaba a jihar Legas, ta gurfanar da wasu daliban kwalejin Dowen biyar da ake tuhuma da laifin kashe Sylvester Oromoni, matashin makarantarsu mai shekaru 12, inda ta bayar da belin su a kan kudi Naira miliyan daya kowanne.
‘Yan sandan sun tuhumi yaran kanana da laifin hada baki da kuma kisan kai
Alkalin kotun, Olatunbosun Adeola, bayan sauraron bukatar neman belin lauyoyin wadanda ake kara, ya umarci wadanda ake kara dasu gabatar da mutane biyu wadanda zasu tsaya masu kowanne a cikin adadin.
Adeola yace daya daga cikin wadanda ake tuhumar dole ne ya zama iyayensu, kuma dole ne ya lashi takobin yin biyayya ga umarnin kotu.
Ta kuma kara da cewa fasfo din kasa da kasa na dukkan wadanda ake tuhuma dole ne a mika su ga kotu, kuma mai gabatar da kara ya tabbatar da inda suke, sannan kuma su kasance a cikin kilomita biyu daga wurin zaman da suke a kowane lokaci.
Lauyoyin dake kare wadanda ake kara, Miss Ifeoma Eson, Mista A.E. Amah, Mista Godwin Omoaka (SAN), Mista Eze Ajibo ya wakilci Begue da Mista Michael Ayinla a gaban kotu kan yaran.
Idan dai ba a manta ba jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a ranar 9 ga watan Disamba ne aka ci gaba da tsare wadanda ake tuhuma a gidan yara kanana bisa zargin kashe abokin karatunsu da aka yi musu a wani lamari na cin zarafi a lokacin da suke makaranta.