Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, ta sake tabbatar da Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Edo a karo na biyu, bayan ya doke abokin hamayarsa na Jam’iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu, a cewar rahoton BBC Hausa.
Wannan ne karo na biyu da Mista Obaseki ke doke Mista Ize-Iyamu, inda a 2016 ma hakan ya faru, amma lokacin Obaseki na APC, Ize-Iyamu kuma a PDP.
Hukumar ta INEC ta bayyana cewa Mista Obaseki ya samu ƙuri’u 307, 955 inda kuma Mista Osagie Ize-Iyamu ya samu ƙuri’u 223,619, rahoton ya ƙara da haka.
Ɗan takarar Jam’iyyar SDP ne ya zo na uku da ƙuri’u 323, sai kuma na Jam’iyyar LP da ya samu ƙuri’u 267.
Hukumar ta ce adadin waɗanda aka tantance domin kaɗa ƙuri’a su ne 557,443, adadin ƙuri’u masu sahihanci kuma 537,407.
https://dimokuradiyya.com.ng/zaɓen-jihar-edo-hotunan-yadda-zaɓen-ke-gudana-a-halin-yanzu/
Adadin ƙuri’un da aka jefa 550,242 sai kuma ƙuri’un da suka lalace a zaɓen 12,835.
‘Yan takara 14 ne suka kara a zaɓen wanda ya gudana a ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2020.
Jihar na da rumfunan zaɓe 3,035 sannan akwai sama da mutum miliyan biyu da aka yi wa rajistar zaɓen, sai dai waɗanda suka jefa ƙuri’ar ba su wuce dubu 600 ba.
Zaɓen Edo dai kamar yadda masana siyasa suka bayyana, tamkar wani zakaran gwajin dafi ne tsakanin APC da PDP da ma ita kanta hukumar INEC.