- Wata kyakkyawar baiwar Allah ta gyara ɗakinta ta kuma saka labule masu tsada wanda ya kai sama da Naira 100,000
- Matar ta ce, duk da ta ga labule masu arha a kasuwa, amma sai ta yanke shawarar sayen wanda ya kai Naira 6,000 a kowace yadi.
- Masu amfani da shafin sada zumuntar Tiktok waɗanda suka kalli bidiyon ta sun yi mamakin cewa labule na iya yin tsada sosai haka, yayin da wasu ke yaba ƙayataccen kayan adon dake cikin ɗakinnata.
Wata budurwa ‘yar Najeriya da ta yi hayar wani gida mai kyau ta yi wa mutane bidiyan ɗakin, inda ta nuna yadda ta samu labule.
Matar ( @victoire_mahounuu ) ta ba mutane mamaki lokacin da ta ce ta kashe Naira 133k a kan labule.
Cikin zolaya tace meyasa bata sayi wanda yafi arha ba. Ta tambaya ko mutanen kauyensu ne suka yanke shawarar zuwa neman labule masu tsada.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata Bazawara Na Neman Mijin Auren Ɗa Shekara 40 Zuwa Sama.
Matar ta ƙara da cewa mai sayar da labule ya ba ta rangwamen kuɗi na N900 akan kowane yadi na labulen N6000.
Maza ne suka saka mata kamar yadda aka gani a cikin bidiyo suna taimaka mata wajen saka su.
Lokacin da aka gama sakawa, matar ta ce tana son yadda ɗakinta ya koma da aka saka labulen.
Majiyarmu ta tattaro wasu daga cikin martanin da akai. Ga wasu a kasa:
@Fhavy ya ce: “Ni mai sayar da labule ne kuma idan na gaya wa mutane cewa labule suna da tsada, ba sa yarda.”
@orjiako Emmanuel ya ce:”Kuna da kuɗaɗen da ke da mahimmanci lallai.”
@nathasiakostand ya ce: “Abu mafi mahimmanci shine ka kashe shi a kan kanka mutuniya ta, kashe kudi a kanka yana da fa’ida sosai.”
@K ya ce: “Ni ma na je na samo labule a makon da ya gabata, 4500 ne a kowane yadi amma kuna na saye shi akan 2800 o.”
@user5222061196739 ya ce: “Kawai ta kira ni Mara Komai a cikin wannan bidiyon naki.”
@Robasil_trends ya ce:”Don labulen taga guda biyu kawai.”
Matar ta amsa da cewa: “Eh.”