- Wata mata ta saki mijinta bayan da ya yi lalata da wata ƙawarta ta Facebook
- Ta ce ta rasa yadda za ta yi da mijinta domin ya ɗauke ta tamkar baiwa
- Kotun ta amince da sakin kuma ta umurci mijin da ya biya diyya
Wata mata dake birnin Livingstone na kasar Zambiya ta saki mijinta da suka shafe shekara 11 bayan ya amince da yin lalata da wata mata da ya haɗu da ita a shafin Facebook.
Prudence Wachama, wacce ta bayyana dangantakarta da mijinta, Presco Lilayi, a matsayin na kanne da ’yar’uwa, ta ce ya ɗauke ta tamkar baiwa a gidanta.
Ta kai karar sa ne a kotun dake Livingstone Local Court A3, inda kotun ta ce ma’auratan sun yi aure a shekarar 2010 kuma Lilayi ya biya K4,500 a matsayin sadaki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Maƙota Sunyi Musayar Matansu Sakamakon Kama Junansu Da Kwartanci
Wachama ta shaida wa kotun cewa ta rasa yadda za ta yi da mijinta, kuma shi bai damu da lafiyarta ba ko da ba ta da lafiya.
Ta kuma zarge shi da samun sakonnin waya daga wasu mata a wayarsa.
Ta ce: “Gaskiya na je wani masauki da wani mutumi da na hadu da shi a Facebook, haduwa kawai muka yi, mun tattauna batutuwan da suka shafi aurena, na gaji da cewa abubuwa suna tafiya dai-dai bayan ba haka ba ne.”
Ta ce ita yanzu ba ta son zama da mijin nata kuma ta yafewa masa saboda halinsa, amma ba za su iya zama tare a matsayin mata da miji ba.
Mahaifin Wachama, Moses Wachama, ya goyi bayan shawarar da ’yarsa ta yanke na kawo karshen auren.
Sai dai Lilayi ya ce har yanzu yana son matarsa kuma baya son a kashe auren.
Ya yarda cewa yana da wata macen a rayuwarsa kuma akwai yawan saƙonnin kar-ta-kwana a wayarsa, amma ya ce wannan ya zama tarihi.
“Bana son auren ya mutu saboda ba zan iya kula da yaranmu ni kaɗai ba, dalilin da yasa take son rabuwa da ni shi ne wani namiji da ta haɗu da shi a Facebook.” yace.
Babban Alkalin Kotun Majistare Fredrick Mainza ya amince da saki kuma ya umurci Lilayi da ta biya K300 a matsayin kuɗin kula da yara.
Ya ce auren ya mai matakin da ba za a iya warwarewa ba kuma babu soyayya tsakanin ma’auratan.
Ya shawarce su da su rika mutunta juna tare da hada ’ya’yansu cikin lumana.