Za a iya cewa ta tabbata ɗan wasan gefe na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid wato Gareth Bale zaibar Real Madrid biyo bayan cimma yarjejeniya da akayi da tsohuwar ƙungiyarsa ta Tottenham dake ƙasaf Ingila.
Za a iya cewa kenan ungulu zata koma gidanta na tsamiya saidai ita Tottenham ta bayyana cewar za’a bata shi a matsayin aro harna tsawon shekara guda.
Bale dai ya kwashe shekaru a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid inda tun a shekarar 2013 yazo wato ya kwashe shekaru bakwai kenan tare dasu.
Idan za a iya tunawa Bale ya bugawa Tottenham wasanni a baya daga shekarar 2007 zuwa 2013 inda ya buga wasanni 146 ya jefa ƙwallaye guda 42.
Idan ba a manta ba a yammacin jiya Tottenham ta sayi matashin dan wasan Real Madrid wato Sergio Reguilon akan £27m inda zai kwashe shekaru 5 tare da su, kuma gashi awanni 8 bayan sayensa sun sake dawo da Gareth Bale.
Bale dai ayanzu shekarsa 31 kuma zaisake dawowa ƙarƙashin mai horas wa Jose Mourinho wanda sunyi aiki tare da she a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid dake ƙasar ta Andalus.