Allah bai halicci baki dan kawai yaci tuwoba, haka Allah bai halicci ni dakai dakeba dan kawai muzama ƙwalliya abisa doron ƙasaba sai dan mu bauta masa., inji Mawaki Zaharaddeen A. Abdallah a yayin zantawar sa da Jaridar Dimokuradiyya
“Ita gaskiya sunanta gaskiya koda abakin mawaƙi tafito, haka kuma ita ƙarya sunanta ƙarya koda daga bakin Malami ta fito.
Acikin Al Qur’ani Allah yagaya mana cewa zai jarabcemu da yunwa, mutuwa, samu dakuma rashi. Dss.
Mutum baya iya sauya ƙaddararsa kamar yanda bai isa yasa ko yahana hukuncin Allah ya tabbata ba.
Dan haka na rungumi ƙaddarata da hannu biyu biyu wata kila bana daga cikin wayanda Allah ya hukuntawa zasuyi aure su haihu a duniya kamar yanda yafaɗa:
Wasu sai yabasu ƴaƴa mata, wasu yabasu maza, wasu kuma yabasu duka maza da mata, wayansu kuma sai ya hanasu duka. Iko nasane mulki nasane, shi yasa yake yanda yaso.
Naji shawarwarinku nagode harda wayanda suka zageni ina godiya agareku duka masoya da maƙiya, ina alfahari daku kuma na yafewa kowa domin rayuwa batayi saida masoya da maƙiya.
Allah ne yabani baiwar waƙa, na ɗauketa sana’a ta rufin asiri kuma zan tsarkake harshena.
Maganar Aure kuma nabarwa Allah komai dama komai ahannunsa yake. ”
Zaharaddeen A. Abdallah +2348036176288
zaabigchief@gmail.com Please 🙏 share, like and comment or suggest.