- Wata kyakkyawar mace ta wallafa bidiyo mai ban sha’awa a shafinta na TikTok yayin da ta cimma burinta na rayuwa
- A cewar matashiyar mai ƙwazo, a koyaushe tana son zama matuƙiyar jirgin sama
- Bayan kimanin shekaru goma na yunƙuri ba dare ba rana, a ƙarshe ta cimma burinta, ta kasance cikin farin cikin
Wata mai amfani da TikTok mai suna @malaikarubani3 ta wallafa abin ban mamaki lokacin da ‘kaftin ɗinga’ ta watsa mata ruwa.
Malaika dai ta riga ta hau kuma ta tuƙa jirginta na farko a matsayin direban jirgi, don haka ne kaftin ɗinta ta yi mata wanka da ruwa.
A cewarta, ta kusa haƙura da burinta na zama matukiyar jirgi amma a karshe ta cimma burinta na tsawon shekaru goma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Maigadi Ya Ɗirkawa Matar Ubangidansa Ciki Har Wata 5.
“POV: Na yi mafarkin zama matukiyar jirgin sama da shekaru goma, kusan sau 1000 ina ƙoƙarin guduwa, amma a yau na tuƙa jirgina na farko matsayin matukiyar jirgi. Allah, don Allah ka yi wa wasu ma abin da ka yi mini.”
Malaika ta kara da cewa kyaftin din nata ita ma tana alfahari da nasarar da ta samu.
Ta rubuta: “Kyaftin ɗina Sharon ta na alfahari da ni hakan yasa tayi min wanka da ruwa.”
Masu amfani da yanar gizo sun shiga sashin sharhi don taya ta murna saboda babban abin da ta samu.
@Jacky ya ce: “Wannan yana da mahimmanci sosai don zai ƙarfafawa wasu gwiwa, ‘yar uwa Allah ya ɗaukaka ku zuwa ga mafi girman nasara.”
@titilope 02 ya amsa: “Barka da warhaka”
@madoka643 ya amsa: “Ina taya ki murna kwarai da gaske…”
@user6379712059400 ya amsa: “Ina tayaki murna da fatan Allah ya kasance a gaba da bayanki, kullum ki hau kuma ki sakko lafiya, ba za ki taɓa samun hatsarin jirgin sama ba, Allah ya kiyaye”.
@chebetfildause390 ya ce: “Allah ya kiyaye kuma amin.”
@ mai amfani111637181613 ya ce: “Naji daɗi ‘yar uwa, Allah ya kara buɗa miki.”
@carolauma472 ya amsa: “Ina taya ki murna ƴar uwa, kin cancanci hakan.”
@Owinolove yayi sharhi: “Ina taya ki murna yarinya ta ina alfahari da ke”.
@Oyindamola ya cd: “Son zama wani abu a rayuwa yana da matuƙar muhimmanci.”