Ta’addanci a Jahar Katsina ya ragu da Kashi 50 a cikin watanni shida da suka gabata — Inji Gwamnati
Mai ba Gwamnan Jahar Katsina Shawara na Musamman akan Tsaro Ahmad Katsina, a ranar Litinin ya bayyana cewar Ta’addancin da ake gudanarwa a Jahar ya ragu da kashi 50 a watanni shida da suka gabata.
Yace ƙididdigar dake ga hannun Gwamnati ya nuna cewa ta’addanci a Jahar ya ragu, yana mai cewa ana cigaba da ɗaukar Ƙarin Matakai domin kare Al’umma.
KARANTA WANNAN LABARIN: KEDCO ta Ƙaryata Zargin Biyan Dubu 27,000 Kuɗin Wutar Lantarki duk Wata a Katsina
Ibrahim Katsina ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga Ƴan Jarida, bayan yayi jawabin taya murna a wajen taron rantsar da wani Kwamiti tsaro domin shigo da Mata a Harkar tsaro mai Suna UNSCR 1325 mai mutum 25 a Katsina.
Yace “a Matsayin ku na Magidanta kunsan cewa akwai zaman lafiya a yanzu a lokuttan nan da suka gabata. Abinda ke garemu shine ta’addanci neman abin ci.
“Daga ƙididdigar dake garemu da kuma bayanan da muke samu a kullum, ya nuna cewa yanayin ta’addancin da ake gudanarwa a Jahar ya ragu da kashi 50 a Jahar.
Ibrahim Katsina yayi nuni dacewar Gwamnati tana shigo da Mata a Harkar magance rashin Tsaro a Jahar, inda muka gano cewa ƴan ta’adda sun fi sauraren Mata a lokacin da suke shawartar su, su daina aikata ta’addanci.
Ya bada tabbacin cewa zaɓen Ƙananan Hukumomi mai zuwa a Jahar, za’a gudanar dashi cikin kwanciyar hankali, yana mai cewa dokar da aka sanya dake hana bangar siyasa a Jahar tana nan.
Maiba Gwamna Shawarar yace “idan ka halarci wani taro na siyasa ko wane iri a jahar a ƴan kwanakin nan, da wuya kaji akwai ƴan bangar siyasa.
“Ya faru ne a dalilin dokar da aka sanya a ƴan kwanakin nan, data hana aikata hakan a Jahar. Hukumomin tsaro an basu damar ɗaukar mataki ga dukkanin wani Ɗan bangar siyasa dake kawo tsaiko ga zaman lafiyar Jahar”.
“Ina mai baku tabbacin cewa babu wata hanya da za’a yi bangar siyasa a zaɓen 11 ga watan Afrilu na Ƙananan Hukumomi da kuma lokacin Babban Zaɓen Shekarar 2023. Muna ƙoƙari domin ganin mun tabbatar da zaman lafiya a Jahar, Insha Allah.”
Babban Sakataren Ma’aikatar Kula da Harkokin Mata na Jahar Abdulhameed Sabuwa ya rantsar da Kwamitin mai mutum 25.