Shugaban kasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier ya nemi gafarar kasar Poland bisa barnar da suka yi mata yayin yakin duniya na biyu shekara 80 da suka gabata, lokacin da bama-baman farko da aka harba a yakin suka fada kan birnin Wielun dake kasar ta Poland.
A waccan lokacin dai Poland ce ta fi kowace kasa fuskantar tashin hankalin yakin duniyar na biyu, la’akari da cewa ‘yan kasar kusan miliyan 6 ne suka halaka a yakin, wanda a jimlace ya yi sanadin mutuwar mutane sama da miliyan 50.
Jimillar adadin kuwa sun hada da Yahudawa akalla miliyan 6, wadanda kusan rabinsu ‘yan kasar ta Poland ne.
A ranar 25 ga watan Agustan da ya gabata, Faransa ta yi bikin cika shekara 75 da kawo karshen mamayar da dakarun sojin Nazi, karkashin Adolf Hitler na Jamus, suka yiwa birnin Paris.
A rana mai kamar ta 25 ga watan Agustan 2019, cikin shekarar 1944, dakarun Faransa da hadin gwiwar ma’aikata, mata, har ma da limaman coci suka samu wannan nasara bayan shafe kwanaki 6 suna gwabza fada da dakarun na Nazi.