Gwamnatin jihar Gombe ta jajantawa Ali Nuhu da ‘yan uwansa bisa rasuwar mahaifinsu, Mista Nuhu Poloma wanda ya taba rike shugaban Jam’iyyar PDP na jihar. Poloma mai shekaru 78 a duniya ya rasu ranar Litinin.
Gwamnatin ta bayyana damuwar tarw da yin jaje ga jarumin masana’antar Kannywood Ali Nuhu da ma ‘yan uwansa na rashin mahaifinsu da suka yi.
Gwamna Yahaya Inuwa, ya bayyana Mista Poloma a matsayin jagora na gari wanda ya yiwa jiharsa da ma kasarsa hidima domin ganin an samu ci gaba.
Gwamnan ya kara da cewa rasuwar Poloma ba wai iya iyalansa ta shafa ba, ta shafi jihar Gombe dama kasar nan baki daya.
Fitaccen jarumin Ali Nuhu, ya godiya a shafinsa na Instagram da irin kauna da jaje da dumbin masoya suka dinga turo masa bisa rasuwar mahaifin nasa.