A cigaba da kai ziyarar ta’aziyya ga Iyalai da ‘yan uwa ns murgayi Sani Dangote، musamman ga gwamnatin jihar Kano da dan uwan murgayin babban dan kasuwan nan Alhaji Aliko Dangote da duk al’ummar jihar baki daya.
Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas, Alhaji Ahmed Bola Tinibu ya zo Jihar Kano domin yin ta’aziyyar rasuwar Alh. Sani Dangote.
Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, da mataimakin sa, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da sauran manyan Jami’an Gwamnati ne suka tarbi jagoran a filin sauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano inda suka wuce gidajen iyalai da yan uwan mamacin domin yi musu ta’aziyya.
Daga nan ne suka wuce fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero domin yi masa ta’aziyya.
A jawabin sa na ta’aziyya Bola Tinubu ya bayyana rashishi a matsayin babban rashi ne da ya shafi kasa baki daya.
Ya kuma bayyana matsayin mutum mai kwazo da aiki akan gaskiya da amana inda yace hakika Allah ne me bayarwa me karba, yayi addu’a akan Allah da ya karbe shi ya bashi Aljannah madaukakiya.