Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yaki da zukar taba sigari, saboda illar da ta ke yi wa bil adama ta fannin lafiya a kowace rana ta Allah.
Bikin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar lafiya ta Duniya ke takun saka da kamfanonin sarrafa tabar sigari, wadanda ke bullo da sabbin dubaru domin janyo hankalin matasa.
Bincike na baya-bayan nan da hukumar lafiya ta duniya ta gudanar, na nuni da cewa akalla mutane milyan 3 da dubu 300 ne ke rasa rayukansu a kowace shekara sakamakon cututuka masu nasaba da zukar taba.
Mafi yawan cututukan na kama huhu ne, yayin da illolin tabar ke shafar hatta yara kanana a cewar masu binciken.