Kungiyar likitoci ta Kasa NARD ta bukaci ma’aikatar lafiya ta tarayya da ta gaggauta daukar mataki kan ‘ daya domin daya’ na maye gurbin likitoci da ma’aikatan jinya da suka fice domin rage karancin ma’aikata a sakamakon matsalar tabarbarewar kwakwalwa kasar.
Kungiyar ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da shugaban ta, Dokta Emeka Innocent Orji ya sanya wa hannu a ranar Lahadi bayan taron majalisar zartarwa ta kasa a Uyo, jihar Akwa-Ibom.
KARANTA HAKANAN Likitocin NARD Suna Barazanar Tafiya Yajin Aiki A Fadin Kasar
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa NARD ta koka da rashin mayar da martani na mafi yawan gwamnatocin jihohi wajen yin amfani da Dokar Horar da Likitoci masu neman kwarewa, 2017, shekaru shida bayan sanya hannu kan dokar.
Ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta fara aiwatar da shirin biyan Asusun Horar da likitoci masu neman kwarewa (MRTF) na shekarar 2023 don baiwa mambobinta damar amfani da kudaden don sabunta kwasa-kwasan watan Fabrairu da jarrabawar Maris da Afrilu da kuma Mayu.
Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta biyan bashin da ake binta na shekarar 2014, 2015 da 2016 da kuma gibin da aka samu a sakamakon daidaita mafi karancin albashi ga mambobin da suka cancanta.
Haka kuma ta bukaci da a gaggauta aiwatar da ayyukan kwamitin da aka kafa domin duba tsarin albashin ma’aikatan lafiya (CONMESS) sannan kuma ya kamata NARD ta ci gaba da gudanar da ayyukanta domin samar da abubuwan da ta ke bukata domin kauce wa sakamakon da ba a so.
Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da kungiyar gwamnonin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki da su yi nasara kan Gwamna Victor Okezie Ikpeazu na Abia da takwarorinsa na Ekiti da Imo da kuma Ondo da su biya abokan aikinsu bashin watanni 25, uku, 10 da biyar.
A Wani Labarin Kuma Hukumar NRC Ta Dawo Da Zirga-zirgar Jirgin Kasan Kaduna-Abuja
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Kasa NRC ta sanar da dawo da ayyukan layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna bayan dakatarwar da aka yi a ranar Juma’a.
Daraktan ayyuka na hukumar, Mista Niyi Alli, a cikin wata sanarwa, ya ce za a fara aiyukan ne a ranar 31 ga watan Janairu.