Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya yi zargin cewa da gangan ne gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele ya aiwatar da manufar musanya kudin Naira a matsayin dabarar yaki da rashin samun tikitin tsayawa takararsa ta shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC mai mulki.
Ganduje ya bayyana haka ne a yayin wani gangamin yakin neman zabe da aka gudanar a Tsanyawa a ranar Lahadi, inda ya gabatar da ‘yan takarar gwamna da mataimakin gwamna na jam’iyyar tare da sauran ‘yan takara ga masu kada kuri’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bankin CBN Ya Yaudari Buhari Akan Sake Fasalin Kudin Naira, Inji Oshiomhole
Gwamnan ya jaddada cewa, “Gwamnan CBN yana yin haka ne kawai domin ya haifar da rudani a zabe mai zuwa ba gaira ba dalili.
“Bai dade cikin jin dadi ba saboda ya kasa samun tikitin takararsa ta shugaban kasa a dandalin babbar jam’iyyar mu ta APC.”
Ya dage cewa gwamnatin jihar Kano da jam’iyyar APC a jihar sun yi adawa da matakin gwamnan CBN.
“Sake fasalin kudin ana yin shi a duk duniya, amma ba kamar yadda muke shaida a kasarmu ba. Lokacin ba daidai ba ne, wa’adin da aka bayar ba daidai ba ne kuma da gangan ne,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, “za mu gayyaci manajojin bankuna nan ba da jimawa ba don yi musu tambayoyi game da karancin sabbin takardun kudi na Naira a bankuna.
“Ya kamata su zo su bayyana mana dalilin da ya sa har yanzu al’ummarmu ke fama da wannan matsala ta canjin Naira. Zan je wurinsu daidaiku don in sa ido kan abin da ke faruwa da kuma dalilin da ya sa.”
A fadar Hakiman Kananan Hukumomin Kunchi da Tsanyawa, ya bukaci shugabannin al’umma da su wayar da kan jama’a a yankinsu don sanar da jama’a cewa, “wahalhalun da jama’a ke fuskanta, Gwamnan CBN ne ya haddasa shi da hannu daya, da gangan ya haifar da rudani a tsarin dimokuradiyyarmu.”
A wani labarin kuma,Godiya Ga Al’ummar Igbo Mazauna Kaduna Bisa Kaunar Da Suka Nuna – Uba Sani
Dan takarar gwamna a jihar Kaduna na jam’iyyar APC kuma Sanata mai ci Sanata Uba Sani ya yabawa yan kabilar Igbo mazauna jihar.
Sanata Uba Sani ya yabawa al’ummar Igbo mazauna Kaduna ya yi wani taron nuna masa goyan bayansu gare shi da takarar da yake yi.