Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ba shi da damar yin nasara a yankin Arewa maso Gabashin kasarnan.
“Hakika dama mu na da yawa sosai kuma muna da karfi a kudurinmu na yin aiki don samun nasarar babbar jam’iyyar mu,” in ji shi.
Gwamna Yahaya ya bayyana haka ne a Minna ranar Asabar lokacin da ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar.
Da aka tambaye shi ko zai goyi bayan dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, wanda dan jam’iyyarsa ne, kan dan uwansa, gwamnan Gombe ya ce babu wani abu kamar dan uwa da jam’iyya, inda ya ce Nijeriya daya ce, don haka sai inda karfinsa ya kare.
KARANTA ANAN: Gwamnatin Kano Ta Shirya Hada Hannu Da Wasu Don Tsaftace Jihar
“Ba komai Atiku daga yanki daya muke tare da shi, Duk ‘yan uwana ne kuma Nijeriya daya ce, muna fafutukar ganin mun ci gaba da rike ta a matsayin kasa daya dunkulalliya da ba za a iya raba ta ba,” inji shi.
Ya kuma bayyana cewa ya je Minna ne domin ziyartar Abdulsalami kan jinyar da ya yi a wani asibitin Burtaniya.
Ya kara da cewa daya daga cikin dalilan da ya sa jihar Gombe ta samu zaman lafiya ciki da kewaye da jihohin da rashin tsaro ke fama da su shi ne yadda suke fahimtar sabanin da ke tsakaninsu da wuri, don ganin an samu maslaha a tsakani.
A wani labarin kuma: Yan bindiga Sun Hallaka Mutum Guda, Tare Da Jikkata Wasu A Kogi
Ana fargabar an kashe mutum daya, yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa ‘yan kasuwa a Ofeapo kan titin Idrisu-Bagana a karamar hukumar Omala ta jihar Kogi.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Wani ganau ya bayyana cewa an yi wa ‘yan kasuwar kwanton bauna ne a yayin da suke komawa gida daga Kasuwar Bagana da misalin karfe 8:30 na daren ranar Alhamis.