Shugaban kwamiitin sojojin ƙasa na Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ali Ndume, ya faɗa wa BBC cewa yanzu suna da ƙwarin gwiwar samun nasara a yaƙi da ta’addanci a ƙasar saboda ƙarin kayan yaƙi da sojoji suka samu.
Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu ya ce binciken da ya yi ya nuna cewa dakarun sojan sama na Najeriya sun samu sabbin jiragen helikwafta fiye da 20.
Ndume na cikin waɗanda ke yawan sukar yadda gwamnatin jam’iyyarsu ta APC ke tunkarar yaƙi da ƙungiyar Boko Haram a lokuta daban-daban a jiharsa ta Borno da yankin arewa maso gabas.
Ya ce kiran da suka daɗe suna yi na ƙara yawan sojoji ya samu karɓuwa, “yanzu za a ɗauki mutum kusan 8,000 saɓanin 4,000 zuwa 5,000 da ake ɗauka”.