Dan wasan Manchester United Jesse Lingard na ci gaba da haskakawa a yan baya bayan nan bayan da kungiyar sa ta tura ahi zaman aro a Kungiyar Westham United.
To sai dai dan wasan ya ce a baya har ya kuduri aniyar barin harkar tamola kachokam din ta bayan da ya gaza gane komai a tawagar United sakamakon yau fari gobe tsumma.
Tun bayan da aka kammala gasar cin kofin duniya ta Shekarar 2018 ne dai al’amurra suka sukurkuce wa Lingard inda har ta kai ga ya gaza samun kanshi a sha dayan farko dake take wasa wa United.
Lingard mai shekara 28 ya shaida wa wata tashar labarai ta YouTube cewa al’amarin ya kai ga ya fara shiga dimuwa indai har ya yanke shawarar barin harkar ƙwallon ƙafa baki daya.
“Na so na yi bankwana da harkar wasanni, wani lokaci haka kawai sai na ji ya kamata a ce na daina kwallo” cewar Lingard.
“To amma yadda na yi ta jajircewa yanzu haka ta san na dawo tamkar mutum.
A Yanzu haka dai Lingard ya samu damar zura kwallaye tara a Ƙungiyar Westham bayan da ya hade da ita a watan Janairu daga United a matsayin aro