- Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta Najeriya ta umurci mambobinta da su koma bakin aiki a yau (Litinin)
- Sai dai NARD ta ce za ta sake duba yajin aikin nan da makonni biyu masu zuwa muddin aka samu tangarda.
- Shugaban kungiyar, Dakta Emeka Orji ya ce an dakatar da yajin aikin daga karfe 8 na safiyar ranar Litinin.
Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta Najeriya ta umurci mambobinta da su koma bakin aiki a yau (Litinin) bayan yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da mambobin kungiyar suka tsunduma a fadin kasar,kamar yadda Punch ta rawaito.
NARD, bayan taronta na musamman na Majalisar Zartarwa ta kasa na tsawon sa’o’i uku, ta ce za ta sake duba kudirin gwamnatin tarayya na warware matsalolin nan da makonni biyu masu zuwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kaso 70% Na Kayan Da Aka Sarrafa Najeriya Ƙasashen Waje Basa Karba – NAFDAC
A ranar Juma’a ne kungiyar ta rattaba hannu kan wata takardar yarjejeniya da gwamnatin tarayya domin magance matsalolin da likitocin masu neman kwarewa suka gabatar.
Sai dai NARD ta ce za ta sake duba yajin aikin nan da makonni biyu masu zuwa.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa idan zaku iya tunawa a ranar 17 ga watan Mayu ne kungiyar NARD ta fara yajin aiki a fadin kasar domin neman gwamnatin tarayya ta amsa bukatunta.
Likitocin na bukatar daukar dimbin ma’aikatan jinya cikin gaggawa a asibitocin; janye kudirin nan na neman tilasta wa daliban da suka kammala karatun likitanci da hakori yin hidimar dole na tsawon shekaru biyar a Najeriya kafin a ba su cikakken lasisin yin aiki.
Kazalika habaka ababen more rayuwa cikin gaggawa a asibitocin tare da raba akalla kashi 15 na kasafin kudi ga lafiya kamar yadda sanarwar Abuja ta 2001 tayi.
Sauran bukatu kuma su ne a gaggauta biyan Asusun Horar da Likitoci masu neman kwarewa a shekarar 2023 daidai da yarjejeniyoyin da aka cimma a taron masu ruwa da tsaki da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta kira a ranar 15 ga watan Fabrairu, 2023.
Sannan nan take aka karawa tsarin albashin Likitoci da ya kai kashi 200 cikin 100 na yawan albashin likitoci baya ga alawus-alawus da ke kunshe cikin wasikar da aka rubuta wa Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire a ranar 7 ga watan Yuli, 2022, don sake dubawa da sauransu.
Shugaban kungiyar, Dakta Emeka Orji, a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya ce an dakatar da yajin aikin daga karfe 8 na safiyar ranar Litinin.
Ya ce kungiyar za ta sake duba irin ci gaban da aka samu dangane da bukatunta a yayin taronta na yau da kullun a Legas.
Orji ya ce, “An dakatar da yajin aikin kuma za a ci gaba da aiki da karfe 8 na safeyar gobe (Litinin yau).
“An tsawaita wa’adin har zuwa 2 ga watan Yuni 2023, don sake tantancewa.”
Sakataren Yada Labarai da Jama’a na kungiyar Dakta Umar Usman ya ce, “Kafin mu fara yajin aikin mun kira taron Majalisar Zartarwa ta kasa kuma majalisar ta ba mu goyon baya kuma mun yi alkawarin cewa za a yi yajin aikin gargadin na tsawon kwanaki biyar.
“Yajin aiki kuma a karshen shi za mu kira su zuwa ga ci gaban da aka samu.
“Don haka gobe za mu koma kamar yadda aka amince. Tunda mun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnati, yarjejeniyar tana da kayyadadden lokaci kuma an amince da cewa za a magance matsalolin akan lokaci.
“Za mu sake nazarin alkawurran da aka yi da kuma sanin ci gaban da aka samu game da batutuwan da aka taso.”
A wani labarin kuma, Jigawa Ta Sanar Da Ranar Fara Jigilar Maniyyatan Jihar
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta tabbatar da cewa jirgin farko na maniyyatan jihar zai tashi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2023 a ranar Asabar 27 ga watan Mayu.
Sakataren zartarwa na hukumar Alhaji Umar Labbo ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Dutse ranar Lahadi. Daily Post ta ruwaito.