An samu tashin hankali a sashin karbar haihuwa na asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi inda aka ce daya daga cikin tagwayen da aka haifa ya bata.
A zantawarsa da Daily Trust, mahaifin tagwayen da aka haifa, Ibrahim Dallami Khalid ya ce wata mata ta shiga dakin da matarsa da tagwayen ke ciki ranar Laraba.
Ya ce matar ta fito a matsayin jami’ar asibitin kuma ta shaida wa matarsa cewa daya daga cikin tagwayen na bukatar magani a wani sashe da ke asibitin, inda ya kara da cewa mayaudariyar ta dauke jaririn bai dawo ba.
Khalid ya ce, “Mun yi zargin wata mata ce ta shiga cikin dakin a lokacin ziyarar, kuma ta gai da duk majinyatan da ke wurin. Na ga matar amma ina tsammanin matata da mahaifiyarta sun san ta.
“Daga baya na bar asibiti, matata ta ce mahaifiyarta ta kawo mata ƙwai. Yayin da take kokarin dauko kwan, sai matar nan ta sake zuwa ta tambayi surukata inda ta dosa. Ta amsa ta fita.
“Matar ta yi amfani da damar ta zauna kusa da matata, ta gaya mata cewa daya daga cikin tagwayen ba shi da lafiya kuma tana so ta kai jaririn wurin kulawa da jarirai na musamman. Matata ta yarda ta dauki jaririn ta bata. Tun daga wannan lokacin, babu wani bayani game da inda jaririn yake. “
KARANTA KUMA: Jariri Dan wattani 19 Ya Fada Rijiya A kano
Da wakilinmu ya nemi jin ta bakin mahaifiyar, Ibrahim ya ce tun da lamarin ya faru ta sume.
Shugaban kwamitin ba da shawara ga likitoci na Asibitin, Dakta Haruna Liman, ya bayyana lamarin a matsayin wani abin takaici.
Ya ce, “An shaida mana cewa mai laifin ta kulla alaka da mara lafiyar da ‘yan uwanta da ke zaune tare da ita kuma ta sa ido sosai kan motsin su.
“Lokacin da mai laifin ta zo daukar daya daga cikin jariran, mahaifiyar ta mika mata yaron kuma babu wanda ya yi zargin wani abu har sai da ta sanar cewa ba a ga jaririnta ba.”
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Shima jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa an fara gudanar da bincike domin cafke wadda ake zargin.
A wani labarin kuma: An Tisa Keyar Farfesar Da Ake Zargi Da Cin Zarafin ‘Yar Sanda Zuwa Gidan Yari
Wata kotun majistare da ke zamanta a Wuse, babban birnin tarayya Abuja, ta tasa keyar Farfesa Zainab Duke Abiola zuwa gidan yari na Suleja bisa laifin cin zarafin sufeto Teju Moses, da ‘yan sanda suka kai karar ta.
An gurfanar da Farfesan ce tare da mai taimaka mata a gida, Rebecca Enechido, ranar Juma’ar nan.