By Abbas Yakubu Yaura
An samu afkuwar wasu fashe-fashe biyu a sansanonin Majalisar Dinkin Duniya a garin Gao dake arewacin kasar Mali a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka yi barna amma ba a samu asarar rai ba, in ji ‘yan jaridar AFP dake wurin.
Fashe-fashen da suka afku da sanyin safiyar lahadi sun girgiza barikin tawagar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali, mai suna MINUSMA, lamarin daya tilastawa mutanen dake cikin mafakar ficewa daga ciki na tsawon sa’o’i biyu.
Sojojin Faransa sun ba da rahoton barnar kaya kawai, amma basu da wani bayani kan yiwuwar wadanda suka kai harin ba.
Mai magana da yawun kungiyar ta MINUSMA Myriam Dessables ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa an kaiwa wasu sansanoni biyu dake arewacin kasar hari a ranar Asabar din da ta gabata, ba tare da wata barna ba.
Tashin hankali na baya-bayan nan a kasar dake yammacin Afirka na zuwa ne bayan an kashe mutane 31 a wani hari da wasu da ake zargin mayakan jihadi ne suka kai ranar Juma’a a kusa da garin Bandiagara dake tsakiyar kasar.
Kasar Mali dai na fafutukar ganin ta shawo kan rikicin ‘yan kishin Islama daya fara barkewa a arewacin kasar a shekara ta 2012, wanda kuma ya yi sanadin mutuwar dubban sojoji da fararen hula.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Duk da kasancewar dubban sojojin Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya rikicin ya mamaye tsakiyar kasar Mali ya kuma bazu zuwa kasashen Burkina Faso da jamhuriyar Nijar dake makwabtaka da kasar.
Kazalika Kasar Faransa wadda itace tsohuwar kasar da ta yiwa Mali mulkin mallaka tace za ta rage yawan dakarunta a yankin Sahel.
Har ila yau, tace tana shirin tura sojoji daga Kidal, Tessalit da Timbuktu zuwa Gao da Menaka, kusa da yankin “iyakoki uku” mai cike da rudani a kusa da Burkina Faso da jamhuriyar Nijar.