Ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich wato Martinez ya kafa tarihi amma tagwaye a gasar ajin ƙwararru ta nahiyar turai wato wasan ƙarshe da ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Bayern Munich ta sha da ƙyar a hannun ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sevilla.
Bayern Munich dai ta lashe kofinne bayan ta doke Sevilla daci 2 da 1 wasan da aka share mintina 90 1 da 1 inda sai a ƙarin mintina 30 da akayi Bayern Munich ta sake jefa ƙwallo ta biyu a raga inda a haka aka tashi daga wasan, sai dai ansha gumurzu sosai da sosai inda saida aka kai ruwa rana sosai abin da ake cewa kare jini biri mini.
Mafi yawan magoya baya a duniyar ƙwallon ƙafa ana zaton cewar za a yiwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sevilla zazzagar ƙwallaye a raga amma sai maganar nan ta tabbata wadda ake cewa ana zaton wuta a maƙera amma sai ta tashi a masaƙa inda da ace nasara tazo tun a dai dai mintina na 88 ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Sevilla zata lashe Bayern Munich amma hakan bata yiwwuba nasarar bata tare da ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Sevilla.
Idan mun dawo maganar tagwayen tarihin da ɗan wasan na Bayern Munich ya kafa wato Martinez wanda shine ya jefa ƙwallo ta biyu a ragar Sevilla, sai dai tagwayen tarihin za a iya cewa ɗaya ya girmi ɗaya da shekaru bakwai inda ya kafa ɗaya a shekarar 2013 sai kuma a jiya ya sake kafa wani a shekarar nan ta 2020 da ake ciki.
Tarihin da ya kafa a shekarar 2013 shine lokacin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich ta saye shi ya jefa ƙwallo a wasan ƙarshe na gasar ta Super Cup na nahiyar turai inda ya jefa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea a wasan ƙarshe wato shekaru bakwai da suka gabata kenan, inda ƙwallon itace ta farko daya jefa a waccan shekarar ta 2013.
Sannan ƙwallon daya jefawa Sevilla a jiya itace ta ƙarshe tunda lokaci yayi dazai bar ƙungiyar domin momawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Athletico Bilbao inda za a iya cewa ƙwallon sa ta farko data ƙarshe a Bayern Munich duka a wasanin ƙarahe na gasar Super Cup ya jefa su.
A wannan sabuwar kakar wasan ta bana dai za a iya cewa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich ta lashe dukkanin kofunan data fafata inda za a iya cewa tayi abin da ake cewa cinye duka kama daga gasar Bundes Liga da gasar zakarun nahiyar turar da gasar ƙalu-bale ta ƙasar Jamus da kuma gasar Super Cup data lashe a daren jiya Alhamis.
A halin yanzu akwai kofi guda ɗaya da ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Bayern Munich ya rage zata fafata shi wato wasan gasar zakarun nahiyoyi, wasan dai ana fafatashi tsakanin ƙungiyoyin da suka zamo zakara a gasar zakaru a nahiyarsu wato nahiyoyi guda bakwai da ake dasu a duniya.
A makon daya gabata aka fara fafata gasar Bundes Liga wato sabuwar kakar wasa ta shekarar 2020 zuwa 2021 inda ƙungiyar ta Bayern Munich ta fara da ƙafar dama bayan data ragargaza ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Schalke 04 daci 8 da nema abin da ake cewa dukan kawo wuƙa kenan. Ana ganin tun a makon farko Bayern Munich ta kama hanyar lashe gasar ta Bundes Liga karo na tara a jere kenan bayan data jera shekaru 8 tana lashe gasar.