By Abbas Yakubu Yaura
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya roki ‘yan Najeriya da kada su goyi bayan ko kuma kada kuri’a ga wasu masu neman shugabancin kasar da suka ce kungiyoyi ne suka siya musu fom din tsayawa takara.
DUBA WANNAN LABARIN: Shugaban Nijar Ya Godewa Najeriya Kan Aikin Gina Layin Dogo Na Sama Da Dala Biliyan 1.96 Daga Kano-katsina-maradi
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito idan zaku iya tuna cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi da sauran yan takara sun yi ikirarin cewa wasu kungiyoyi sun sayi fom din tsayawa takara a jam’iyyarsu ta PDP agare su.
Sai dai Obasanjo, wanda ya yi magana a lokacin wani taro na bikin cika shekaru 61 na Fasto Itua Ighodalo a Legas, ya ce masu son yi wa ‘yan Najeriya karya ne, don haka bai kamata a zabe su a zaben shugaban kasa mai zuwa ba.
Tsohon shugaban kasar, wanda ya yarda cewa matsalar kasar nan ta samo asali ne daga rashin shugabanci nagari.
Sannan ya bayyana cewa matasa ba za su iya biyan fam din tsayawa takara na Naira miliyan 40 ba kamar yadda masu son tsayawa takara ke ikirari.
Ya ce, “A yau suna biyan Naira miliyan 40 Wasu daga cikinsu (masu son tsayawa) sun ce wasu matasa ne suka saya musu.
“A gaskiya, duk wanda zai fito fili ya yi maka irin wannan karya, bai kamata ka zabe shi ba. Wadanne matasa ne suka tara Naira miliyan 40? Idan kana so ka saya, sayi ka gaya mana. Ba ka bukatar ka yi mana karya.”
Our medulla oblongata are working 24/7 needs no anyone to give us a hints for our future… Together we can make it,,,
We’re NIGERIA ‼️‼️