By Abbas Yakubu Yaura
Shahararren dan gwagwarmayar zamantakewa da siyasa kuma tsohon dan majalisar tarayya, Shehu Sani, ya gargadi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da kada ya bari “a yaudare shi”.
Shehu Sani ya yi wannan gargadin ne a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook ranar Litinin.
Gwamnatin Imo Zata Gudanar Da Jana’izar Mutanen Da Fashewar Haramtacciyar Matatar Mai Ta Shafa
Gargadin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa Jonathan zai sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki tare da bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasa a 2023.
Ya rubuta, “Kada GEJ ya yaudari kansa kuma kada ya bari a yaudare shi.”
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Juma’ar da ta gabata ne Jonathan ya shaida wa magoya bayansa da suka yi dafifi a ofishin gidauniyar sa da su sanya ido a kan tunkarar zaben 2023.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a Abuja a lokacin da yake jawabi ga magoya bayansa, galibinsu matasa da mata, wadanda suka yi kira gare shi da ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.
Jonathan ya bayyana sarai cewa tsarin siyasa game da shawararsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ya riga ya ci gaba.