An samu tashin gobara a sabon reshen majalisar wakilai a yammacin ranar Alhamis din nan, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Daraktan yada labarai na majalisar, Agada Rawlings Emmanuel, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce gobarar ta afku ne a daya daga cikin ginin ma’aikatan gidan da ke hawa na 2, daki na 227 a sabuwar majalisar wakilai.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Ya ce ana zargin gobarar ta samo asali ne daga matsalar wutar lantarki da daya daga cikin ma’aikatan ya lura da shi ga magatakardar Majalisar Wakilai, wanda ba tare da bata lokaci ba ya sanar da hukumar kashe gobara ta tarayya da ke a harabar Majalisar.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/buhari-ya-sha-alwashin-ceto-mutanen-da-aka-yi-garkuwa-da-su-a-kaduna/
“Haka zalika, an kashe gobarar tare da taimakon ma’aikatan da ke bakin aiki inda nan take suka kutsa cikin ofishin da abin ya shafa tare da tura na’urorin kashe gobara a kasa kafin isowar jami’an kashe gobarar.
“Saboda haka, hadin gwiwar da aka yi cikin gaggawa, an shawo kan gobarar a ofishin da abin ya shafa tare da kashe wutar lantarki ga reshen don ba da damar tantancewa da bincike kan lamarin.
“Ana sa ran cewa, bayan tantancewar da hukumar kashe gobara da kuma daraktocin ayyuka suka yi, komai ya daidaita a sabon ginin, gidajen duk manyan jami’an majalisar wakilai da na ofishin Honorabul za a dawo dasu nan take.
“Hukumar gudanarwa na son yabawa cikin gaggawa da mayar da martani kan matakan da masu bayar da gudunmawa na farko suka yi musamman, ma’aikatan majalisar dokoki ta kasa da sashin kashe gobara wajen taimakawa wajen dakile barkewar gobarar,” in ji shi a cikin wata sanarwa.
(DAILY TRUST)