Hukumar Kula da’ar ma’aikata ta jihar Kano, CSC ta kori wasu ma’aikata hudu a jihar Kano bisa samunsu da laifin mallakar takardun bogi da bayar da bayanan karya.
A cikin wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na hukumar ta CSC, Ismail Garba Gwammaja ne ya fitar, inda ya ce, shugaban hukumar Bello Mohammad Kiru ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis jim kadan bayan kammala taron da hukumar ta saba yi na horar da manyan ma’aikata.
Kazalika ya Kuma bayyana cewa, a halin yanzu, CSC ta amince da karin girma ga ma’aikata 126 a cikin ma’aikatan gwamnati.