Yayin da ake ci gaba da neman hanyar magance annobar Korona, yanzu matsalar dake addabar jama’a musamman talaka ita ce mawuyacin halin rayuwa, da suka haɗa da rashin kuɗi da kuma tsadar rayuwa ta kayan masarufi.
Kawo yanzu gwamnatin tarayyar da kuma jihohi na iƙirarin kashe dubban Miliyoyin Naira wajen tallafawa masu ƙaramin ƙarfi, domin rage raɗaɗin wahalar rayuwa da ake fama da ita sakamakon annobar Korona.
Ahmad Tukur Jada, ɗaya daga cikin shugabanin ƙungiyoyin ƙananan manoma a Najeriya, ya bayyanawa wakilinmu irin ƙalubalen da talakawa ke fuskanta a wannan lokaci na annoba, wanda ya haɗa da tsadar rayuwa. Game da batun tallafin Korona kuwa ya ce babu abin da suka gani.
Sai dai yayin da talakawa ke kokawa, tuni wasu wakilai da kuma ƙungiyoyi suka fara neman hanyar tallafawa, domin ragewa al’umma wahalar da suke ciki.
Muhammad Auwal, wanda yana ɗaya daga cikin shugabanin ƙungiyoyin masu zaman kansu a jihar Kano, yace iri-iren tallafin da gwamanti ta bawa talakawa ya yi kaɗan kuma daga ƙarshe ma an samu wasu sun karkatar da wasu daga cikin kayan, daga ƙarshe ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi duba da irin halin matsi da talaka ke fuskanta a faɗin ƙasar nan.